Isa ga babban shafi

An gwabza kazamin fada tsakanin bangarorin 'yan bindiga biyu a Zamfara

‘Yan ta’adda da dama sun mutu a wani kazamar fada da ya barke tsakaninsu a kauyen Hayin Alhaji da dajin Munhaye na karamar hukumar Tsafe a jihar Zamfara ta arewacin Najeriya.

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

Rahotanni sun bayyana cewa gwabzawar ta faru ne a sakamakon yunkurin da wasu ‘yan bindiga daga jihar Katsina suka yi na yin garkuwa da wasu mazauna kauyukan Zamfara a karshen makon nan.

A cewar rahotannin bayan da 'yan bindigar na Katsina suka mamaye kauyukan na Zamfara ne, kasurgumin dan bindigar nan na jihar Ado Alero ya yi gaggawar kai wa kauyukan dauki don dakile yunkurinsu na satar jama'a.

Shaidun gani da iso sun tabbatarwa manema labarai cewa a wannan yunkuri an gwabza kazamin fada tsakanin bangarorin biyu wanda ya kai ga asarar rayuka, duk da cewa dai bangaren Ado Alero sun dakile shirin garkuwa da mutanen kauyen.

A halin yanzu, bayanai sun ce mazauna kauyukan da aka gwabza kazamin fadan sun shirya gudanar da birne gawarkin 'yan ta'addan da suka mutun, wadanda har zuwa yanzu ba a kai ga tantance adadinsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.