Isa ga babban shafi

Mayakan sa kai sun kashe 'yan bindiga 50 yayin arangamarsu a jihar Sokoto

Mayakan sa kai a jihar Sokoto ta Najeriya sun tabbatar da kisan ‘yan bindiga akalla 50 yayin wata arangama tsakaninsu da ta kai ga rasa rayukan mayakan na sakai 12.

'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya. © Leadership
Talla

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa ‘yan sa kan sun yi kokarin dakile yunkurin ‘yan bindigar na farmakar wasu kauyuka a jihar Sokoto ta arewacin kasar a Lahadin da ta gabata, wanda ya kai ga arangamar.

Yankunan arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya na ganin hare-haren ‘yan bindiga da ke kai hare-hare tare da sace mutane don neman fansa wanda a lokutan da dama sukan kashe mutanen da basu ji ba basu gani ba.

Mayakan ‘yan sa kan wanda bayanai ke cewa an kwaso sune daga yankin arewa maso gabashin Najeriyar don yakar matsalar ta ‘yan bindiga a jihohin na arewa maso yamma da tsakiyar kasar bayan da suka shafe shekaru 14 suna yaki da mayakan Boko Haram.

A zantawarsu da AFP jagoran ‘yan sa kan Babakura Kolo ya ce sun kashe ‘yan bindigar akalla 50 ko da ya ke an kashe musu mutane 12.  

A cewar jagoran ‘yan sa kan galibin ‘yan bindigar da suka kashe yaran rikakken dan fashin dajin nan ne Bello Turji, wadanda suka yi kaurin suna wajen kai wa kauyuka hare-hare tare da kisan tarin mutane baya ga sata da aikata fyade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.