Isa ga babban shafi

Najerira: An kama dan bindigar da ake zargi da kashe Nabeeha

Rundunar 'Yansandan Najeriya ta tabbatar nasarar da ta cimma ta damke shahararren dan bindigar da ake zargi da Kashi Nabeeha daya daga cikin matan da suka yi garkuwa dasu a Abuja babban birnin kasar. 

'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya
'Yan bindiga sun addabi jihar Zamfara ta Najeriya © dailypost
Talla

 

Wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya tabbatar da cewa yana daga cikin gungun wadanda suka yi garkuwa da su Nabeeha da mahaifinta sannan suka kashe Nabeeha da wasu waɗanda suka sace.

An sace 'yan matan shida ne da mahaifinsu ranar 2 ga watan Janairun 2024.

 

Rundunar ƴan sandan Nijeriya ta tabbatar da kama wani dan bindiga wanda ake zargi da kashe matashiyar nan Nabeeha da kuma garkuwa da wasu.

Rundunar ta tabbatar da hakan ne a wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi inda ta ce ta kama ɗan bindigar a wani otel da ke garin Tafa a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

A sanarwar, ta ce dan bindigar mai shekara 28 mai suna Bello Mohammed asalin dan jihar Zamfara ne kuma an kama shi da zunzurutun kudi har naira miliyan 2.25, inda ake zargin kudin fansa ne da ya karba.

“Wanda ake zargin a lokacin da ake yi masa tambayoyi, ya tabbatar da cewa yana daga cikin gungun wadanda suka yi garkuwa da wani Barista Ariyo a unguwar Bwari da ke Abuja a ranar 2 ga watan Janairun 2024, inda suka kashe wasu daga cikin wadanda suka yi garkuwa da su, daga ciki har da Nabeeha, wadda ƴa ce ga lauyan, a ranar 13 ga watan Janairun 2024 a sansanin masu garkuwan da ke Jihar Kaduna.

"Wanda ake zargin, a cikin wani yanayi mai ban mamaki, ya bayar da naira miliyan 1,000,000 don jawo hankalin wani babban jami’in ‘Yansada wato DPO, wanda ya ki amincewa da tayin, inda ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata," in ji sanarwar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.