Isa ga babban shafi

Najeriya:'Yan bindiga da dama sun mutu a arangama da sojoji a Mangu ta Filato

Rahotanni daga Najeriya na sun ce ‘yan bindiga da dama ne suka mutu sakamakon wata  aranagama tsakanin su da sojojin kasar a wasu kauyuka na karamar hukumar Mangu ta jihar Filato dake arewa  maso tsakiyar kasar da safiyar Asabar din nan.

'Yan bindiga da dama sun mutu a arangama tsakaninsu da sojoji a karamar hukumar Mangu.
'Yan bindiga da dama sun mutu a arangama tsakaninsu da sojoji a karamar hukumar Mangu. RFI
Talla

Wasu majiyoyi daga yankin sun ce ‘yan bindiga 30 ne aka kashe a wannan fada da aka gwabza a kauyukan Satguru da Tyop, a yayin da wasu dakarun kasar suka samu raunuka.

Wata majiya ta tsaro da ta nemi a sakaya sunanta ta ce wannan fadan ya  barke ne da misalin karfe 7 zuwa karfe 7 da rabi na safiyar Asabar din nan ne, bayan da ‘yan bindigar da suka fito da dimbim yawa suka afka wa wasu kauyuka a kan hanyar Gindiri, kuma nan take aka shaida wa jami’an tsaro, wadanda ba su bata lokaci ba suka kai dauki.

Bayan kashe 30 daga cikin ‘yan bindigar, sojin Najeriya sun kama 50  daga cikinsu da rai, kana suka kwace dimbim makamai da suka hada da bindigogi da harsasai.

Har yanzu dai babu wani karin bayani daga  runduna ta musamman da ke samar da tsaro a yankin Filato, wato Operation Safe Haven.

Wannan arangamar na zuwa ne bayan da gwamnan jihar Filato Caleb Mutfwang ya sassauta dokar hana fita ta tsawon sa’o’i 24 da ya kakaba wa ilahirin karamar hukmar ta Mangu, yana mai cewa sassaucin ya zama wajibi ne  ganin yadda aka samu daidaituwar al’amura, bayan rikicin da ya barke a yankin a farkon wannan makon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.