Isa ga babban shafi

Dubban mutane sun yi zanga-zangar adawa da kashe-kashen Bokkos a jihar Filato

A wannan litinin dubban mutane ne suka gudanar da tattaki a garin Jos fadar gwmanatin jihar Plateau da ke Najeriya, inda suke nuna takaicinsu a game da hare-haren da aka kai yankin Bokkos da Barikin Ladi tare da samun asarar rayukan sama da mutane 10 kimanin makonni biyu da suka gabata. 

Yadda wani hari ya salwantar da rayukan tarin mutane a jihar Pulato ta Najeriya.
Yadda wani hari ya salwantar da rayukan tarin mutane a jihar Pulato ta Najeriya. AP - APTN
Talla

Mafiya yawan wadannan suka gudanar da tattakin na yau na sanye  ne da bakaken tufafi wanda ke alamta cewa suna zaman makoki da kuma juyayi ne sanadiyyar wadannan hare-hare da suka haddasa asarar rayukan mutane masu tarin yawa. 

Masu tattakin sun zagaye wasu titunan birnin Jos, kafin daga karshe su gudanar da taron gangami a harabar ginin daya daga cikin kananan hukumomi da ke birnin, inda suka gabatar da jawabai da ke yin kira da a samar da tsaro da kuma dawo da zaman lafiya a tsakanin al’ummomin da ke rayuwa a jihar. 

Reverend Stephen Baba Panya, wanda ya jagoranci wannan gangami, ya bayyana cewa fatansu shi ne kawo karshen tashe-tashen hakula da kuma kashe-kashen da ke faruwa a jihar, inda ya ce babu yadda za a samu iya nasarar wanzar da zaman lafiya a jihar face an dauki matakin baza dimbin jami’na tsaro musamman a yankunan da suka yi kaurin suna wajen tashe-tashen hankula. 

A ranar 23 ga watan disambar da ya gabata, ‘yan bindigar wadanda har yanzu mahukuntan jihar basu kai ga sanr da duniya daga inda suka fito, suka kaddamar da farmaki kan kauyuka da dama, inda akalumma da mahukuntan jihar Plateau suka fitar ke cewa akalla mutane 198 ne suka rasa rayukansu, yayin da aka lalata dukiya mai tarin yawa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.