Isa ga babban shafi

'Yan bindiga sun tarwatsa wani sansanin soji a Katsina

Wani gungun ‘yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai farmaki kan wani sansanin soji da ke kauyen Nahuta a karamar hukumar Batsari ta jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya.

'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya.
'Yan bindiga sun addabi wasu yankuna a jihohin Najeriya. © Leadership
Talla

Mazauna yankin sun ce da misalin karfe 11 da rabi na daren Lahadi ne wannan gunnu na ‘yan bindiga suka suka kai wannan samame a kan sojojin da aka jibge don samar da tsaro a yankin.

Ko da ya ke dakarun da ke wannan sansani sun dakile harin, ‘yan bindigar sun samu nasarar kona motocin soji 2 tare da lalata wasu kayayyaki a sansanin.

Duk da yadda ‘yan bindigar suka fito da dimbim yawa a yayin samamen, babu wanda ya mutu a cikin sojojin Najeriya, kamar yadda rahotanni suka nuna.

Rahotanni sun ce maharan sun yi amfani da damar da rudanin harin da suka kai ya samar wajen kai hari a garin Nahuta, inda suka fasa shaguna da gidaje, suka kuma yi awon gaba da kayayyakki na makudan kudade.

Wata majiyar soji ta ce ‘yan ta’addan da suka kai wannan samame a kan sansanin soji sun zarce 100, kuma sun banka wa wasu motocin soji biyu wuta.

Rahotanni sun ce bayan harin ana iya ganin dimbim jama’a daga garin Nahuta suna arcewa saboda fargabar abin da zai je ya zo, inda wasu daga cikin su suka nemi mafaka a garin Batsari da kauyen Wagini.

Babu wani bayani a hukumance daga rundunar sojin Najeriya da na ‘yan sandan jihar Katsina ya zuwa lokakcin hada wannan rahoto.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.