Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Sabuwar gwamnatin Katsina ta sha alwashin magance matsalar tsaro

Wallafawa ranar:

Sabuwar gwamnatin jihar Katsina ta Najeriya da ta yi rantsuwar kama-aiki a wannan Litinin ta bayyana sabbin matakan da za ta dauka wajen magance matsalar tsaro, wadda ta yi sanadiyar mutuwar mutane da dama tare durkusar da tattalin arzikinta. 

Sabon gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Radda
Sabon gwamnan jihar Katsina Dakta Dikko Radda © Daily Trust
Talla

Katsina na daya daga cikin jihohin arewacin Najeriya da ‘yan bindiga ke cin karansu babu-babbaka, amma sabuwar gwamnatin ta ce, lallai tana da dabarun da za ta yi amfani da su wajen shawo kan matsalar. 

Wakilinmu na Abuja Mohd. Sani Abubakar ya tattaunawa da sabon gwamnan jihar, Dakta Dikko Radda. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.