Isa ga babban shafi

Najeriya: Kotu a Barno ta bada umurnin sakin mutane 313 da ake zargi da ta'addanci

A Najeriya wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Borno ta bayar da umarnin sakin mutane akalla 313 da ake zargin ƴan ta’adda ne da sojoji suka kama.

Mayakan Boko Haram
Mayakan Boko Haram AFP
Talla

Kotu ta bayar da umarnin a sake su ne saboda rashin shaidar da za ta sa a yi musu hukunci.

Hakan na zuwa ne yayin da hedkwatar tsaron Najeriya ta ce, sojojin sun kashe ƴan ta'adda 121, tare da kama 253 da kuma kubutar da mutane 244 da aka yi garkuwa da su a wasu samame daban-daban da suka kai a cikin mako guda.

Daraktan yaɗa labarai na ma’aikatar tsaro, Manjo Janar Buba Edward ne ya bayyana haka a yayin taron manema labarai kan ayyukan soji a fadin kasar ranar Alhamis a Abuja.

Buba ya ce za su bi umurnin kutun wajen mika mutanen ga gwamnatin Barno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.