Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotu ta goyi bayan daurin shekaru 25 ga 'yan Boko Haram

Kotun daukaka kara da ke birnin Legas a tarayyar Najeriya ta goyi bayan hukuncin daurin shekaru 25 ga wasu mutane uku da ake zargin alakarsu da kungiyar Bokom Haram.

Wasu daga cikin mayakan kungiyar Boko Haram
Wasu daga cikin mayakan kungiyar Boko Haram Youtube
Talla

Wata sanarwa da gwamnatin Legas ta fitar ta ce, mai shari’a Ibrahim Buba ne ya tabbatar da goyon bayan hukuncin wanda babbar kotun tarayya ta yanke a cikin watan Satumba shekara ta 2014.

Kotun ta samu Ali Muhammad Madu da Adamu Ali Karumi da Ibrahim Usman Ali da laifin cin amana da ayyukan ta’addanci da kuma boye bayanai har ma da mallakar miyagun makamai bayan an tuhume su a watan Maris na shekarar 2013.

An dai yanke hukunlci a asirce ne saboda tsaro kamar yadda hukumomi suka ce, yayin da kungiyoyin fararen hula suka bukaci a gudanar da shi a bainal jama’a.

Rikicin kungiyar Boko Haram wanda ya fi tsananta a yankin arewa maso gabashin Najeriya, ya kashe mutane akalla dubu 20 yayin da  kusan miliyan 3 suka rasa muhallansu.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.