Isa ga babban shafi
Nijar

Boko Haram ta kashe sojojin Nijar

Sojojin Nijar guda bakwai sun rasa rayukansu sakamakon hare-haren da kunggiyar Boko Haram a ta kai musu a makon jiya, abinda kuma ya raunata takwas daga cikinsu.

Boko Haram ta kashe sojojin Nijar bakwai a Diffa
Boko Haram ta kashe sojojin Nijar bakwai a Diffa ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Kungiyar ta kai hare-haren ne a yankin yamma maso gabashin jihar Diffa da ke kan iyaka da Najeriya kamar yadda sanarwar rundunar ta sanar.

A farkon watan nan ne, Boko Haram ta kashe mutane biyar a yankin na Diffa wanda kuma shi ne farmaki na farko da kungiyar ta kaddamar tun daga watan Yuni da ya gabata.

Rikicin Boko Haram ya yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 20 a Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru, yayin da mutane fiye da miliyan 2 suka rasa muhallansu.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.