Mayakan Boko Haram sun kashe mutane 5 a Tumur dake Diffa a Nijar.
Rahotanni daga kauyen Tumur dake kusa da Bosso a jihar Diffa na kasar Janhuriyar Nijar na cewa ‘yan kungiyar Boko Haram sun kai wani kazamin hari inda suka kashe mutane biyar da kona gidaje shida
Wallafawa ranar:
Majiyoyin samun labarai na cewa yammacin jiya Juma'a aka kai wannan hari duk da cewa jami'an tsaro na iyakacin kokarin kawo karshen ayyukan hashsha da ‘yan kungiyar ke yi a yankunan.
Yanzu haka dai jami'an tsaro daga kasashen Najeriya, Nijar, Kamaru da Chadi na iyakacin kokari ne domin kakkabe guggubin ‘yan kungiyar Boko Haram da suke hana sukuni a kauyukan dake kan iyakokin kasashen yankin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu