Isa ga babban shafi
Nijar

Kungiyar Boko Haram tana zafafa kai hari a Nijar

Wasu masu bincike kan harkar tsaro, sun bayyana cewa Jamhuriyar Nijar na ci gaba da zama dandalin kai hare haren kungiyar book haram, sakamakon matsin lambar da kungiyar ke samu a Najeriya, da kuma rikicin shugabancin da ya addabe ta.  

Wasu daga cikin jami'an tsaro da ke sintiri a kusa da jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar
Wasu daga cikin jami'an tsaro da ke sintiri a kusa da jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar Nicolas Champeaux pour RFI
Talla

Masanan sun ce yayin da hare haren kungiyar ke raguwa a Najeriya, akwai fargabar samun karuwar su a Jihar Diffa dake Nijar.

Roddy Barclay dake kungiyar Africa Practice yace karancin tsaro akan iyaka da kuma yadda ‘ya’yan kungiyar ke sajewa cikin jama’a na daga cikin matsalolin da ake fuskanta.

Sai dai kuma wata majiya daga mahukuntar jihar ta Diffa ta ce a halin da ake ciki jihar bata fuskantar wata barazanar tsaro, kuma jama'a suna cigaban da harkokinsu kamar yadda suka saba, zalika ayyukan gwamnati na cigaba da gudana.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.