Isa ga babban shafi
Nijar

Sabuwar kungiyar ta'addanci ta yi barazanar kai hari Nijar

Wata Sabuwar kungiyar 'Yan ta’adda a Nijar ta yi barazanar kaddamar da hare hare a Yankunan da ake hakar ma’adinin uranium da ke arewacin kasar saboda abinda suka kira bam-bamcin da ake nunawa 'yan kabilar su ta Toubou.

Sojojin Najeriya da ke bayar da tsaro a Yankin Bosso dake Nijar
Sojojin Najeriya da ke bayar da tsaro a Yankin Bosso dake Nijar AFP
Talla

Adam Tcheke Koudigan da ya kira kan sa shugaban sabuwar kungiyar ta ‘Movement for Justice and the Rehabilitation of Niger’, wato kungiyar da ke bukatar ganin anyi gaskiya da sake gina Nijar, ya ce za su dauki makamai dan yakin da zai kai su kwato hakkokin su.

Koudigan ya ce gwamnatin Nijar ta yi watsi da bukatun su da kuma kare yankin su da ake hako ma’adinai, inda ya zargi kamfanin hakar man China da tara miliyoyin daloli yayin da su suke fama da talauci.

Jami’in a wani faifan bidiyo ya ce suna nan suna shiri, kuma idan lokaci ya yi za su kaddamar da hare haren su a kasar.

Sai dai gwamnatin kasar ta yi watsi da bidiyon da kungiyar ta raba wanda ta bayyana shi a matsayin farfaganda.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.