Drogba da Mikel da Yaya Toure da Song suna cikin wadanda CAF za ta zaba gwarzon Afrika
Hukumar CAF da ke kula da kwallon kafa a Nahiyar Afrika ta fitar da jerin sunayen ‘Yan wasa 10 da zata zaba gwarzon Afrika a bana. ‘Yan wasan sun hada da dan wasan Kamaru Alexander Song da ke taka kwallo a kungiyar Barcelona a Spain. Akwai dan wasan kasar Ghana Andre Ayew da ke taka leda a kungiyar Marseille ta Faransa.
Wallafawa ranar:
Akwai kuma Christopher Katongodan dan wasan kasar Zambia da ke taka kwallo a kungiyar Henan Contruction ta kasar China. Sai kuma Demba Ba dan kasar Senegal da ke wasa a kungiyar Newcastle United.
Akwai sunan Didier Drogba na cote d’Ivoire da ke wasa a kungiyar Shaghai Shehua ta kasar China. Akwai kuma Lombe Yao Kouassi shi ma dan wasan Cote d’Ivoire ne da ke taka kwallo a kungiyar Arsenal ta Ingila.
Akwai dan Najeriya John Obi Mikel da ke taka kwallo a kungiyar Chelsea mai rike da kofin gasar zakarun Turai.
Akwai kuma Yaya Toure na Cote d’Ivoire da ke wasa a Manchester City wanda aka zaba gwarzon afrika a bara. Sai Younes Belhanda na Morroco da ke taka leda a kungiyar Montpellier ta Faransa.
Kafin karshen watan Nuwamba ne dai za’a tankade ‘Yan wasa bakwai a fitar da sunayen ‘Yan wasa uku wadanda cikinsu ne za’a zabi gwarzon Afrika a bana a watan Disemba a birnin Accra na kasar Ghana.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu