Isa ga babban shafi
CAF

Senegal za ta fuskanci fushin CAF bayan tayar da rikici a filin wasa

Mai horar da ‘Yan wasan kasar Senegal Ferdinand Coly yace ya zama dole kasar Senegal ta amince da duk wani hukunci da hukumar CAF z ata yanke bayan ‘Yan kallo sun tayar da rikici a filin wasan birnin Dakar a lokacin da suka sha kashi hannun Cote d’Ivoire.

Rikicin kwallon Kafa a Senegal
Rikicin kwallon Kafa a Senegal Reuters/Mamadou Gomis
Talla

‘Yan kallo dai sun yi amfani da duwatsu da kwallabe suna jifar ‘Yan wasan Cote D’Voire bayan zira kwallaye biyu a ragar Senegal.

Amma har yanzu hukumar CAF ba tace komi ba, amma Mista Ferdinand yace ya zama dole Senegal ta amince da duk matakin da hukumar zata dauka.

Masu kula da sha’anin kwallon kafa dai a Afrika sun yaba da yadda ‘Yan wasan Cote d’Ivoire da magoya bayansu suka kama jikinsu ba tare da sun abka cikin rikicin ba Bayan da aka kama jifar su. Kamar yadda Ministan cikin gidan Senegal ke cewa ya zama dole su nemi afuwar Cote d’Voire.

Kasashen da dai suka tsallake zuwa gasar cin kofin Afrika da za’a gudanar a kasar Afrika ta kudu sun hada da Algeria da Angola da Burkina Faso da Cape Verde da Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo da Habasha da Ghana da Cote d’Ivoire da Mali da Morocco Nijar da Najeriya da Afrika ta Kudu mai masaukin baki da Togo da Tunisia da Zambia.

Kasar Cape Verde ce dai ta haramtawa kasar Kamaru tsallakewa a gasar duk da cewa kamaru ce ta samu nasara da ci 2-1 amma a karawar Farko Cape Verde ta samu nasara da ci 2-0.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.