Isa ga babban shafi

Biden ya sake taimakawa Isra'ila da makaman sama da dala biliyan 2.5

A cikin 'yan kwanakin nan Amurka ta ba da izinin mika bama-bamai da jiragen yaki na biliyoyin daloli ga Isra'ila, kamar yadda wasu majiyoyi biyu da ke da masaniya kan yunkurin suka bayyana a ranar Juma'a, duk da cewa Washington ta fito fili ta bayyana damuwarta game da harin da sojojin Isra'ila ke shirin kai wa Rafah.

Shugaban Amurka Joe Biden ya halarci wata ganawa da Firanministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, yayin da yake ziyara a Isra'ila kan rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Hamas. 18/10/23.
Shugaban Amurka Joe Biden ya halarci wata ganawa da Firanministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, yayin da yake ziyara a Isra'ila kan rikicin da ke tsakanin Isra'ila da Hamas. 18/10/23. © Evelyn Hockstein / Reuters
Talla

A cewar majiyoyin, sabon kunshin makaman da kudinsu ya haura dala biliyan 2.5 sun hada da bama-bamai sama da 1,800 kirar MK84 da bama-bamai 500 kirar MK82, kamar yadda jaridar Washington Post ta tabbatar.

Kasar Amurka na ba da tallafin soji na dala biliyan 3.8 ga Isra'ila da ta kasance daɗeɗɗiyar kawarta.

Amurkawa na adawa da matakin

Wannan kunshin ya zo ne a daidai lokacin da Isra'ila ke fuskantar kakkausar suka daga kasashen duniya kan ci gaba da kai hare-hare ta sama da kasa a Gaza da kuma yadda wasu 'yan jam'iyyar shugaba Joe Biden ke kira gare shi da ya yanke taimakon da Amurka ke ba wa sojojin Isra’ila.

Amurka dai na ci gaba da taimakawa Isra’ila sosai a yankin da ta ke yi da Hamas, sai dai wasu 'yan jam'iyyar Democrats da na Larabawan Amurka sun soki yadda gwamnatin Biden ke nuna goyon baya ga Isra'ila, wadda ke bata damar cin karenta babu babbaka ba tare da an hukunta ta ba.

Damuwar Biden

A ranar Jumma’a, shugaban Biden ya damu yanayi da Amurkawa da yawa ke ji game da yakin Gaza da kuma goyon bayan Amurka ga Isra'ila, amma, ya sha alwashin ci gaba da marawa Isra'ila baya duk da rashin jituwar da ke tsakaninsa da firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a baya-bayan nan.

Fadar White House ta ki cewa komai kan batun sabon ƙunshin makaman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.