Isa ga babban shafi

Biden ya isa Isra'ila bayan harin da ya kashe mutane a asibitin Gaza

Shugaban Amurka Joe Biden ya isa kasar Isra’ila a yau Laraba, inda ake sa ran zai tattauna da Fira Minista Benjamin Netanyahu, a kokarinsa na amfani da hanyar diflomasiya wajen dakile fadadar yakin da ya barke tsakanin Isra’ila da kungiyar Hamas.

Shugaban Amurka Joe Biden bayan sauka a Tel Aviv babban birnin Isra'ila. 18 ga Oktoba, 2023.
Shugaban Amurka Joe Biden bayan sauka a Tel Aviv babban birnin Isra'ila. 18 ga Oktoba, 2023. AP - Evan Vucci
Talla

Sai dai a halin yanzu za a iya cewa shirin shugaban na Amurka ya gamu da cikas sakamakon harin Isra’ila da ya kashe akalla mutane 500 a asibitin Al-Alhali Baptist da ke kudancin Gaza.

Da fari dai an tsara cewar bayan kammala ziyara a Tel Aviv, Biden zai yi tattaki don tattaunawa da shugaban Falasdinawa Mahmud Abbas da kuma sauran shugabannin kasashen Larabawa da suka hada da Jordan da Masar, amma jagororin suka soke ganawar ta keke da keke, bayan fusata su da Isra’ila ta yi.

Amurka dai ta sha nanata goyon bayan Isra’ila kan ‘yancin kare kan da ta ce tana da shi, koda yake shugaba Biden yace ba zai goyi bayan mamaye Zirin Gaza ba, zalika dole ne a kiyaye rayukan fararen hula.

Sai dai ko a ranar Talata gabanin tashin shugaban zuwa birnin Tel Aviv, rundunar sojin Amurka ta bayyana ware dakarun dubu 2 cikin shirin ko ta kwana, kan yiwuwar aikewa da su yankin Gabas ta Tsakiya, domin taimka wa Isra’ila idan bukatar hakan ta taso.

Shugaban Amurka Joe Biden tare da Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv. 18, Oktoba 2023.
Shugaban Amurka Joe Biden tare da Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a birnin Tel Aviv. 18, Oktoba 2023. REUTERS - EVELYN HOCKSTEIN

Yayin ganawa da Fira Ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, Biden ya ce:

Na damu  matuka da harin da aka kai kan asibitin Gaza a jiya, kuma daga abinda na gani, alamu sun nuna cewar daya bangaren ne suka kai harin amma ba ku ba.

A halin da ake ciki Falasdinawa sama da 3,000 suka mutu a hare-haren Isra’ila ke kai wa Gaza, tun bayan farmakin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga watan Oktoba, wanda ya kashe mutane sama da 1,400.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.