Isa ga babban shafi

Biden zai ziyararci Isra’ila don goyon bayan yakin da take yi da Hamas

Gobe Laraba ake sa ran shugaban Amurka Joe Biden zai kai ziyara Isra’ila don jaddada goyon bayansa ga kasar kan yakin da take yi da kungiyarsa Hamas, yayin da kuma ya ba da umarnin ware wasu dakaru na musamman don taimaka wa Isra’ilar idan bukatar hakan ta taso. 

shugaban Amurka Joe Biden zai kai ziyara Isra’ila.
shugaban Amurka Joe Biden zai kai ziyara Isra’ila. REUTERS - ELIZABETH FRANTZ
Talla

Gabanin ziyarar ta Biden, rundunar sojin Amurka ta sanar da ware dakaru dubu 2 wadanda ke ci gaba da kasancewa cikin shirin tura su yankin gabas ta  tsakiya don taimaka wa Isra’ila idan bukatar hakan ta taso. 

Duk da cewar a ranar Lahadin da ta gabata, Biden yayi gargadin cewa kuskure ne babba idan har Isra’ila ta kai ga mamaye Zirin Gaza, shugaban na Amurka ya nanata cewar kasar na da ‘yancin kare kanta daga barazanar mayakan Hamas, kungiyar da ya ce kamata yayi a shafe ta daga doron kasa, to amma dole ne baiwa yankin Falasdinu ‘yancin zama kasa. 

Isra’ila ta shafe kwanaki 10 tana kai hare-hare  ta sama kan Zirin Gaza, lamarin da yayi sanadin mutuwar Falasdinawa kusan dubu 3, matakin da ke a matsayin martani  kan farmakin da Hamas ta kai mata a ranar 7 ga wannan wata na Oktoba, da ya kashe mata mutane kusan dubu 1 da 500. 

A daren jiya Litinin Isra’ila ta kai sabbin hare-haren da suka kashe mutane akalla 71 a garuruwan Khan Younis da Rafa da suke kudancin Zirin Gaza, inda Falasdinawa ke dauka a matsayin tudun mun tsira, bayan tserewa daga arewacin yankin. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.