Biden na ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya
Shugaban Amurka Joe Biden ya fara ziyarar a yankin Gabas ta Tsakiya daga kasar Isra’ila, inda a ganawarsa ta farko da shugabannin kasar, suka sha alwashin hada karfi domin fuskantar babbar abokiyar hamayyarsu Iran.
Wallafawa ranar:
Tuni dai ta bayyana cewa, tattaunawar Biden da shugabannin Isra’ila za ta fi mayar da hankali ne kan Iran, kamar yadda mai rikon kwaryar mukamin Fira Minista kasar ta Isra’ila Yair Lapid ya tabbatar, a lokacin da ya tarbi shugaban Amurka a filin jirgin sama.
A ranar Juma’a ne kuma ake sa ran Biden zai yi tattaki zuwa Saudiya, inda ake sa ran sai gana da shugabannin kasar kan kokarin kulla kyakkyawar alaka tsakaninsu da Isra’ila, kasar da har yanzu masarautar ba ta amince da wanzuwarta ba.
Masu sharhi dai na ganin ko shakkah babu, ziyarar da Biden ke yi a Isra’ila za ta sake fusata shugabannin Falasdinawa, wadanda suke tuhumar Amurka da gazawa wajen dakatar da cin zalin da Yahudawa ke yi musu.
Shi kuwa shugaban Iran Ibrahim Raisi gargardin shugaban Amurka yayi kan cewar babu yadda za a yi ya cimma burin karfafa tsaron Isra’ila domin tabbatar da fifikonta a gabas ta tsakiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu