Isa ga babban shafi
Amurka - Isra'ila - Iran

Kasashen Isra’ila da Amurka sunyi barazanar amfani da karfin tuwo kan Iran

Kasashen Isra’ila da Amurka sunyi barazanar dawo da tsarin amfani da karfin tuwo kan kasar Iran matukar bata daina jan kafa kan dakatar da samar da makamashin nukiliyar da ta ke yi da gangan ba.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antoni Blinken da takwaransa na Isra'ila Yair Lapid, 27 ga watan Yuni shekarar 2021.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antoni Blinken da takwaransa na Isra'ila Yair Lapid, 27 ga watan Yuni shekarar 2021. AFP - ANDREW HARNIK
Talla

Barazanar kasashen biyu na zuwa ne a wani taro tsakanin firaministan Isra’ila Nefthali Beneth da sakataren harkokin wajen Amurka Antoni Blinken da kuma hukumomin hadaddiyar daular larabawa.

Wannan barzana ta su na zuwa ne dai-dai lokacin da ake ci gaba da kwangaba kwan baya game da sake kulla yarjejeniyar nukiliyar Iran da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya yi fatali da ita.

To amma kasashen na zargin ita Iran da jan kafa da gan-gan saboda bata son sake kulla makamanciyar yarjejeniyar da kowacce kasa, wanda kuma hakan ne ya tunzura kasashen.

A cewar Yair Lapid ministan harkokin wajen Isra’ila duk wasu matakai da Iran din ke bukatar a cika, kasashen sun cika, amma tana ci gaba da kawo wasu dalilai na ba gaira babu dalili da zasu kawo tsaiko game da lamarin.

Shi kuwa a jawabin sa Antoni Blinken na Amurka shawartar mahukuntan Iran din ya yi da su bada kai bori ya hau, matukar ba haka ba kuma to amfani da karfin tuwo akan ta ya zama dole.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.