Isa ga babban shafi
Iran-Nukiliya

Iran ta sanar da shirin fara tace kashi 60 na sinadarin uranium

Hukumar da ke yaki da yaduwar makamin nukiliya ta duniya ta IAEA ta ce hukumomin Iran sun sanar da ita cewar za su fara shirin ta ce kashi 60 na sinadarin uranium kwanaki biyu bayan ta zargi Isra’ila da kai mata hari cibiyar makamashinta da ke Nantaz.

Kashi 90 na makamashin uranium Iran ke bukata gabanin fara iya amfani da shi a bangaren Soji don mallakar makamin na Nukiliya.
Kashi 90 na makamashin uranium Iran ke bukata gabanin fara iya amfani da shi a bangaren Soji don mallakar makamin na Nukiliya. AP - Vahid Salemi
Talla

Kafofin yada labaran Iran sun ce a wasikar da gwamnatin kasar ta rubutawa Hukumar IAEA mai dauke da sanya hannun Abbas Araghchi, mai taimakawa ministan harkokin wajen kasar ta fanni siyasa, ta ce kasar za ta fara tace kashi 60 na sinadarin ba tare da bayyana lokacin farawa ba.

Masana na cewa yin hakan zai bai wa kasar damar samun kashi 90 na makamashin wanda ake iya amfani da shi ta hanyar soji.

Kasar Amurka da Israila da kuma kawayenta su sun sha alwashin cewar ba za su bari Iran ta mallaki makamin nukiliyar ba, abinda ya sa a shekarar 2015 manyan kasashen Duniya cikin su har da Faransa da Birtaniya da Jamus da Rasha da China da Amurkar da kuma Majalisar Dinkin Duniya da kasashen Turai suka kulla yarjejeniyar da za su hana kasar samun makamin, yayin da a bangare daya kuma za su taimakawa kasar samun bukatun ta na makamashi.

Yarjejeniyar ta samu koma baya lokacin da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya janye kasar sa daga cikin ta, kafin zuwan shugaba Joe Biden da ya bayyana komawa ciki.

A makon jiya bangarorin biyu sun gudanar da taro, wato tsakanin Iran da wakilan kasashen Faransa da Birtaniya da Jamus da China da Rasha da kuma wakilan Majalisar Dinkin Duniya da na Turai domin ceto yarjejeniyar.

Iran ta sha alwashin ba zata koma mutunta yarjejeniyar ba muddin Amurka bata cire mata takunkuman da ta dorawa kasar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.