Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Tattaunawar Iran da Amurka kan nukiliya na samun nasara

Daya daga cikin manyan jami’an Diflomasiyyar Rasha dake cikin tattaunawar da ake yi kan farfado da yarjejeniyar nukiliyar Iran ya ce kwalliya na biyan kudin sabulu, ko da yake za a iya daukar lokaci, kafin kammala cimma samun nasarar kan ganawar.

Bushehr, babbar tashar tace makamashin Uranium domin shirin nukiliyar Iran dake kudancin birnin Teheran.
Bushehr, babbar tashar tace makamashin Uranium domin shirin nukiliyar Iran dake kudancin birnin Teheran. ASSOCIATED PRESS - Vahid Salemi
Talla

Yau Talata aka gudanar da taron tattaunawa kan shirin nukiliyar Iran tsakanin kasar da kuma Amurka wadda ake fatan ta koma cikin yarjejeniyar da tsohon shugaba Donald Trump ya yi fatali da ita a 2018.

Taron dai na gudana ne karkashin sanya idanun kasashen Turai, a birnin Vienna.

Tuni dai shugaban Amurka Joe Biden ya ce a shirye yake ya gudanar da tattaunawa da Iran din da kuma amincewa da duk wasu hanyoyi da za a samar da za su inganta alaka tsakaninsu.

Sai dai Iran ta ce babu wani abu dai zai sanya ta amince da duk wani shirin Amurka na tattaunawa da ita, matukar bata janye takunkuman karya tattalin arzikin da ta kakaba mata ba, a don haka tace dole ne kasashen Turai, su tabbatar da hakan.

Sai dai tun kafin taron tattaunawar ta yau, wakilin Amurka a wajen Taron Rob Maley ya ce, Amurka na sha’awar gyara alaka tsakanin ta da Iran, a don haka ba ta da wani dalili da zai hanata janye takunkuman.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.