Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Nukiliya: Iran ta bukaci janye takunkuman dake kanta a lokaci guda

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce kasar ba za ta amince da matakin bi daya bayan daya ba, wajen janye takunkuman da tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya kakkaba mata a shekarar 2018, domin komawa mutunta yarjejeniyar nukiliyar ta.

Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani.
Shugaban kasar Iran Hassan Rouhani. AP - Ebrahim Noroozi
Talla

A baya dai Iran ta amince da shirin na bi daya bayan daya wajen janye mata takunkuman a sannu, amma ta sauya matsayinta, bayan da sabon shugaban Amurka Joe Biden ya shafe watanni ba tare fara aiwatar da matakin ba.

Yayin ganawa da manema labarai a jiya, kakakin ma’aikatar harkokin wajen Iran Sa’eed Khatib-zadeh ya ce ya zama dole a cirewa kasar dukkanin takunkuman dake kanta a lokaci guda, kafin ta koma mutunta yarjejeniyar nukiliyar.

A shekarar 2018 tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya janye daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, tare da  lafta mata takunkuman karya tattalin arziki, bayan zargin cewar yarjejeniyar na cike da kura-kurai, matakin da ya haifar da tsamin danganta tsakanin kasashen 2.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.