Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Takunkuman Amurka sun janyo mana hasarar dala tiriliyan 1 - Iran

Iran tace matakin yin gaban kai wajen sake lafta mata takunkuman karya tattalin arziki da Amurka ta yi a zamanin gwamnatin Donald Trump, ya yiwa tattalin arzikinta mummunar illa, bayan tafka hasarar akalla dala triliyan 1.

Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif
Ministan harkokin wajen Iran Mohammad Javad Zarif REUTERS/Evgenia Novozhenina
Talla

Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Javad Zarif ya bayyana hakan, yayin wata ganawa da kafar PressTV a yau lahadi.

Zarif ya ce da zarar sabon shugaban Amurka Joe Biden ya janye takunkuman, tare da komawa cikin yarjejeniyar nukiliya ta shekarar 2015, ya zama dole Iran din ta tattauna da Amurkan kan biyanta diyyar hasarar da ta tafka, a dalilin sake lafta mata takunkuman karya tattalin arzikin da aka yi.

A shekarar 2018 tsohon shugaba Trumpn ya janye Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar Iran, tare da sake lafta mata takunkuman karya tattalin arziki, wadanda ministan harkokin wajen kasar Javad Zarif yace yawansu ya kai 800.

Ministan yace ya zama dole Amurkan ta janye dukkanin takunkuman kafin sake komawa yarjejeniyar da ta fice daga cikinta shekaru 2 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.