Isa ga babban shafi
Iran-Amurka

Iran ta sabunta kiran ganin Amurka ta janye mata takunkumai

Iran ta sabunta kira ga Amurka wajen ganin shugaba Joe Biden ya yi amfani da damar da ya ke da ita wajen janye takunkuman karya tattalin arziki da Donald Trump ya mayarwa kasar.

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani.
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani. © AFP
Talla

A wani sako da ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya wallafa a Twitter, ya ce kasar a shirye ta ke ta dakatar da bunkasa shirinta na mallakar makamin Nukiliya matukar Amurka za ta janye takunkuman ba tare da sanya wasu sharudda ba.

A jiya Alhamis Joe Biden ya mika bukatar sabuwar tattaunawa da Iran bisa jagorancin Turai a kokarin janye matakin da Trump ya dauka kan kasar da nufin ceto yarjejeniyar Nukiliyar 2015 da ke kokarin rugujewa.

Tuni sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken ya bayyana matakin Iran na sanya wa’adin Lahadi mai zuwa a matsayin ranar karshe da za ta ci gaba da biyayya ga dokokin Majalisar Dinkin Duniya kan makamin nukiliya a matsayin mai cike da hadari.

Jim kadan bayan ganawar Blinken da takwarorinsa na kasashen Birtaniya Jamus da Faransa, daraktan siyasa na EU Enrique Mora ya aikewa kasashen Iran da Amurka bukatar gayyatar zama a teburin tattaunawa don samo mafita kan halin da ake ciki da nufin ceto yarjejeniyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.