Isa ga babban shafi
Iran-Belgium

Belgium ta aike da jami'in Diflomasiyyar Iran gidan yari na shekaru 20

Kotu a Belgium ta yanke hukuncin daurin shekaru 20 kan wani jami’in diflomasiyyar Iran bayan samunsa da laifin yunkurin kai harin bam kan wani gangamin siyasa a wajen birnin Paris cikin shekarar 2018, farmakin da aka dakile.

Assadollah Assadi Jami'in Diflomasiyyar Iran da kotu ta samu da laifin yunkurin tayar da bom a Faransa.
Assadollah Assadi Jami'in Diflomasiyyar Iran da kotu ta samu da laifin yunkurin tayar da bom a Faransa. NCR
Talla

Zaman yanke hukuncin da ya karfafa tsamin dangantaka tsakanin Turai da Iran ya gudana ne cikin tsauraran matakan tsaro a birnin Antwerp.

Kotun ta Belgium ta kuma daure wasu abokan Assadi 3 tsakanin shekaru 15 zuwa 18, tare da kwace takardun shaidarsu na zama ‘yan kasar.

Tuni dai jam’iyyar adawar kasar Iran ta NCRI da ke gudun hijira, wadda kuma akai yi yunkurin kaiwa taron nata farmakin na bam a 2018, ta bayyana hukuncin daurin na shekaru 20 kan Assadollah Assadi a matsayin gagarumar nasara.

Bayanai sun nuna cewar Assadi wanda jami’I ne a ofishin jakadancin Iran dake Austria, ya aike da bama-bamai don kai farmaki kan taron jam’iyyar adawar ta NCRI a Faransa ne ranar 30 ga watan Yuni na shekarar 2018.

Jami’an tsaron Belgium sun dakile harin ne bayan kame motar dake dauke da bama-baman, kwana guda kuma bayan haka suka kame Assaudollah Assadi a Jamus, inda aka haramta mishi amfana da samun kariyar zamansa jami’in Diflomasiya na kasa da kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.