Isa ga babban shafi
Iran

Mun fasa korar jami'an nukiliya daga kasarmu-Iran

Shugaban Iran Hassan Rouhani ya bayyana cewa, kasar a shirye take ta yi zaman tattaunawa da Hukumar da ke Sanya Ido kan Makamashin Nukiliya ta Majalisar Dinkin Duniya, a daidai lokacin da Faransa ta sanar cewa, Amurka da kasashen Turai za su gana da mahukunatan Tehran.

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani.
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani. Official Presidential website/Handout via REUTERS
Talla

Shugaba Rouhani ya jaddada cewa, Iran ta fasa korar Jami’an Hukumar Kula da Makamashin Nukiliya kamar yadda ta yi alwashi da farko, kuma za ta ci gaba da aiki tare da hukumar a yanzu.

A can baya dai, Iran ta ce, muddin Amurka ta ki janye takunkumin da aka kakaba mata karkashin mulkin Donald Trump, to lallai , za ta hana Hukumar Kula da Makamashin ziyarar sanya ido a wasu cibiyoyinta da suka hada da sansanonin sojinta da ake zargi da sarrafa nukiliya.

Wannan matakin ya tsananta damuwar kasashen duniya game da yiwuwar korar jami’an da ke sanya ido kan nukiliyar Iran din, abin da ka iya zama babban koma-baya ga yarjejeniyar da Tehran ta cimma da manyan kasashen duniya a shekarar 2015.

Sai dai a yanzu, gwamnatin Rouhani ta nanata cewa, yanzu haka ba ta da niyar hana jami’an Hukumar Makamashin gudanar da aikinsu na bincike a kasar.

A bangare guda, Faransa ta ce, za ta shirya zaman tattaunawa a gobe Alhamis tsakanin jami’an diflomasiyar manyan kasashen Turai da kuma Sakataen Harkokin Wajen Amurka Anthony Blinken, inda za su mayar da hankali kan batun na Iran.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.