Isa ga babban shafi
Amurkaa-Iran

Biden ya gindaya wa Iran sharadi kafin janye mata takunkumai

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce, ba zai janye takunkuman da ke kan Iran ba muddin ta ci gaba da karya ka’idojin yarjejeniyar nukiliyar da ta cimma da manyan kasashen duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump a fadar White House
Shugaban Amurka Donald Trump a fadar White House REUTERS/Kevin Lamarque/File Photo
Talla

A lokacin da aka tambayi Biden a yayin wata hira da kafar CBS kan ko zai dakatar da takunkuman da aka kakaba wa Iran domin shawo kan kasar don ganin ta dawo teburin tattaunawa, sai ya kada baki ya ce, A ‘a.

Sai dai shugaban na Amurka ya nuna cewa, za su samu jituwa da Iran da zarar kasar ta daina habbaka makamashin Uraniun dinta.

Sai dai a jiya Lahadi, shugaban juyin juya halin Musuluncin Iran, Ayatollah Ali Khamenei ya ce, dole Amurka ta fara janye daukacin takunkuman kafin ita kasar ta koma mutunta ka’idojin da aka shimfida mata.

Yarjejeniyar ta nukiliyar Iran ta fara tangal-tangal ne tun dai lokacin da tsohon shuagaba Donald Trump ya janye Amurka daga cikinta a 2018, yayin da kuma
Amurkar ta sake laftawa Tehran takunkumi.

Shekara guda bayan matakin na Trump, Iran ta jingine mutunta ka’idojin yarjejeniyar ta nukiliyar da aka cimma a shekarar 2015.

Tuni gwamnatin Biden ta bayyana aniyarta ta sake shigar da Amurka cikin yarjejeniyar , amma ta hakikance cewa, sai fa Tehran ta ci gaba da mutunta ka’idojin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.