Isa ga babban shafi
Amurka

Trump ba zai rika samun bayanan sirri kan tsaro ba - Biden

Shugaban kasar Amurka Joe Biden yace tsohon shugaba Donald Trump ba zai dinga samun bayanan asiri daga hukumomin tsaro ba, kamar yadda aka saba baiwa tsaffin shugabanin kasa saboda halayen sa na rashin tabbas.

Shugaban Amurka Joe Biden.
Shugaban Amurka Joe Biden. Joshua Roberts / Reuters
Talla

Biden yace bai ga dalilin da zai sa Trump ya dinga samun wadannan bayanai na asiri ba, saboda ba zai iya rike su a matsayin sirri ba, wanda hakan ke nuna cewar yana iya bayyana su ga jama’a.

Shugaban yace bayanan asirin ba zasu kara ma Trump komai ba, sai dai bashi damar tsegunta su ga jama’a.

Wannan zai zama karo na farko da za’a daina baiwa tsohon shugaban kasa irin wadannan bayanai na asiri domin sanin halin da kasar ke ciki.

Kasar Amurka na da al’adar gabatar da bayanan tsaro na sirri ga tsoffin shugabannin domin sanin halin da ake ciki a koda yaushe.

A shekaru 4 da yayi a karagar mulki, Donald Trump yayi ta takun saka da hukumomin tsaron kasar, abinda ya sa ya sauya shugabannin hukumar leken asirin kasa har sau 6.

Trump ya kuma ki amincewa da rahotan hukumar leken asirin kan cewar kasar Rasha tayi katsalandan a zaben shekarar 2016 wanda ya bashi damar samun nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.