Isa ga babban shafi
AMurka-Yemen

Ya dace a kawo karshen yakin Yemen-Joe Biden

Shugaban Amurka Joe Biden ya ce kamata ya yi a kawo karshen yakin da ake yi a Yemen, yana mai alkawarin dakile dukkanin gudummawar da kasarsa ke bai wa dakarun da Saudiyya ke jagoranta a Yemen, tare da dakatar da sayar da makamai.

Sabon shugaban Amurka Joe Biden
Sabon shugaban Amurka Joe Biden Angela Weiss / AFP
Talla

Makonni biyu bayan rantsuwar kama aiki, Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris sun yi tattaki zuwa Ma’aikatar Harkokin Wajen kasar a wani mataki na nuna goyon baya ga aikin da jami’an diflomisiyya ke yi.

A jawabin da ya gabatar, Biden ya ce a kokarin da su ke na jaddada kudirinsu, za su kawo karshen goyon bayan da Amurka ke badawa a yakin da ake a Yemen, ciki har da sayar da manyan makaman yaki.

Wannan mataki ya warware manufar tsohon shugaba Donald Trump na samar da taimakon kayan aiki tare da sayar da dimbim manyan makaman yaki, kamar makamai masu linzami ga hadakan mayakan da Saudiya ke jagoranta.

Sabon shugaban na Amurka ya shaida wa ma’aikatan diflomasiyyan irin mahimmancin da suke da shi a cikin kudirorinsa, yana mai cewa diflomasiyya ta dawo.

‘Yan tawayen Huthi na Yemen, ta bakin wani babban jami’insu, Hamid Assem sun jinjina wa Biden a kan wannan mataki, inda Assem din ya ke cewa an dau hanyar kawo karshen yakin da aka dade ana yi a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.