Isa ga babban shafi
Iran-Nukiliya

An kaiwa cibiyar tace makamashin nukiliyar Iran farmaki

Iran ta ce an kai harin ta’addanci ta’addanci kan tashar nukiliyarta ta Natanz.

Cibiyar tace makamashin nukiliya na Uranium a yankin Natanz dake kasar Iran.
Cibiyar tace makamashin nukiliya na Uranium a yankin Natanz dake kasar Iran. © Raheb Homavandi / Reuters
Talla

Iran ta fitar da sanarwar ce sa’o’i kalilan bayan da ta bayyana lamarin a matsayin hatsari wanda ya kai ga katsewar lantarki a yankin na Natanz.

Cikin sanarwar da ya fitar, shugaban Sashin Nukiliya na Iran, Ali Akbar Salehi ya bukaci kasashen Duniya su kalli farmakin a matsayin ta’addanci neman dakile sashin ko kuma kokarin Iran na mallakar ciakakkiyar fasahar sarrafa makamashin Nukiliya.

Akbar Ali ya kuma dora alhakin harin kan masu adawa da Iran ta fuskar siyasa addini da kuma mu’amala baya ga kokarin dakile mata ci gaba, ko da ya ke bai fayyace sunan kasar da yake zargi ba.

Jim kadan bayan da Iran sanar da kai mata farmakin, Isra’ila wadda ke matsayin babbar abokiyar gabar ta, ta fitar da sanarwar cewa a shirye ta ke ta hada hannu da Amurka wajen ceto yarjejeniyar nukiliyar ta 2015 wadda yanzu haka ake ci gaba da tattaunawa akanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.