Isa ga babban shafi

Shugaban Amurka Joe biden yayi gaban kansa wajen sayarwa Isra'ila makaman yaki

Karo na biyu cikin wata guda, gwamnatin Amurka karkashin jagorancin shugabanta Joe Biden ta yi gaban kanta wajen sayarwa da Isra’ila manyan makamai cikin gaggawa dai-dai lokacin da take ci gaba da barin wuta kan Zirin Gaza.

Shugaba Biden ne ya amince da sayar da makaman bisa radin kansa
Shugaba Biden ne ya amince da sayar da makaman bisa radin kansa AP - Andrew Harnik
Talla

Wannan na nufin shugaban ya sayar da makaman ba tare da jin ra’ayin majalisa ba, kamar yadda yake bisa dokokin kasar.

To sai dai kuma bayanai sun ce sakataren harkokin wajen Amurkan Antoni Blinken ya baiwa ‘yan majalisar labarin cewa gwamnatin ta sayarwa da Isra’ila makamai kan kudi har dala miliyan 147.5 wadanda suka hadar da manyan bindigogi, makamai masu linzami da sauran kayayyakin kayi.

Yayin da yake jawabi gaban majalisar Antoni Blinken ya ce la’akari da bukatar gaggawa da Isra’ila ke da shine ya tilasta sayar mata da makaman ba tare da neman shawarar ‘yan majalisar ba.

 

Ya ce Amurka ta damu matuka da harin da Hamas ta kaiwa Isra’ila don haka zata yi duk mai yiwuwa wajen ganin ta taimaka mata don kare kanta.

Ko a ranar 9 ga watan Disamban da muke ciki sai da gwamnatin Amurkan ta sayarwa da Isra’ila makamai kan dala miliyan 106, wadanda suka hadar da tankokin yaki guda dubu 14 da miliyoyin alburusai.

Duk wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da Amurkan ke shirin samar wa da Ukraine kayan tallafi da makamai da darajar kudin su ta kai dala miliyan 106, da kuma wasu kayan tallafi suma da kudin su ya kai dala biliyan 14.3 ga yankin gabas ta tsakiya musamman yankin Gaza.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.