Isa ga babban shafi

WFP na bukatar dala miliyan 242 don tallafa wa dubban 'yan gudun hijira a Chadi

Hukumar Samar da Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya WFP, ta ce cikin watan gobe tallafin abincin da ake bai wa dubun dubatar ‘yan gudun hijirar Sudan da ke kasar Chadi zai yanke, muddin ba a samar da kudaden cigaba da ayyukan na jin kai ba.

Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da yakin Sudan ya raba da muhallansu.
Wasu daga cikin dubban 'yan gudun hijirar da yakin Sudan ya raba da muhallansu. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Tun bayan barkewar kazamin yaki tsakanin sojojin gwamnati da ‘yan tawayen RSF kusan shekara guda da ta gabata, ‘yan Sudan sama da dubu 500 suka tsere zuwa Chadi, inda a yanzu haka kididdiga ta nuna cewar kasar na karbar bakuncin ‘yan gudun hijira sama da miliyan guda, abinda ya sanya ta zama daya daga cikin yankunan nahiyar Afirka da ke kan gaba wajen yawan mutanen da tashin hankali ya raba da muhallansu.

Cikin rahoton da ta fitar a baya bayan nan, hukumar WFP ta ce yanzu haka kalubale babba take fuskanta wajen ciyar da dubban ‘yan gudun hijirar, lamarin da ya tilasta wa adadi mai yawa daga cikinsu rasa damar cin abinci a wasu lokutan.

Wani abin tayar da hankali da hukumar samar da abincin ta bayyana kuma shi ne yadda kusan rabin daukacin yara kanana daga cikin ‘yan gudun hijirar kasar ta Sudan ke fama da matsalar rashin isasshen jini, saboda rashin samun isasshen abinci mai gina jiki.

A takaice dai hukumar ta WFP ta ce dala miliyan 242 take bukata domin cigaba da aikin isar da tallafin abinci ga dubban ‘yan gudun hijirar da ke Chadi har zuwa watanni 6 nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.