Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta ce Sudan ce kasa ta daya da jama'arta suka fi fama da yunwa

Majalisar dinkin duniya ta ce Sudan na gab da zama kasa mafi fama da yunwa sanadin yaki a duniya, bayanin da ke zuwa bayan watanni 11 da fara yakin kasar.

Yakin Sudan na gab da shiga shekara guda, kuma har yanzu rayukan mutane na cikin hadari.
Yakin Sudan na gab da shiga shekara guda, kuma har yanzu rayukan mutane na cikin hadari. AFP - HASSAN ALI ELMI
Talla

Rikicin da ke tsakanin Jagoran gwamnatin sojin kasar Abdulfattah AlBurhan da shugaban rundunar kai daukin gaggawa ta RSF Mohammed Hamdan Daglo ya lakume rayukan dubban mutane tare da rusa kasar da kuma durkusar da tattalin arzikin ta.

Yakin na watanni 11 ya raba mutane sama da miliyan 8 da muhallan su, abinda ya sanya yakin matsayin wanda ya fi kowanne haddasa hijira a duniya.

Da take jawabi shugaban hukumar samar da abinci ta majalisar dinkin duniya Cindy McCain ta ce a yanzu yunwa itace babbar barazanar da fararen hula a Sudan ke fama da ita.

Shekaru 20 da suka gabata yankin Darfur shine mafi fama da tsananin yunwa sanadin yaki a duniya, sai dai yanzu akwai yiwuwar yankin yayi kunne doki da Sudan din kan ta.

McCain ta nuna takaicinta kan yadda duniya ta manta da Sudan da irin tsanannin da fararen hular kasar ke ciki duk a sakamakon yakin da za’a iya magance shi ta hanyar tatttaunawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.