Isa ga babban shafi

Ya kamata a kawo karshen rikicin Sudan cikin gaggawa - MDD

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres, ya bukaci bangarorin da ke rikici da juna a Sudan da su amince da batun tsagaita wuta a lokacin azumin watan Ramadan, matakin da kwamitin sulhun Majalisar ke nazari a kai, yayin da kasashen duniya ke ci gaba da nuna damuwa kan halin da fararen hula ke ciki a kasar.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres
Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gutteres TONY KARUMBA / AFP
Talla

Antonio Guterres, ya ce a halin yanzu akwai babban hatsarin cewa rikicin na iya haifar da rashin zaman lafiya tun daga yankin Sahel zuwa kuryar gabashin Afirka da kuma tekun Bahar Rum.

Kwamitin Sulhun na Majalisar Dinkin Duniya ya ce zai tattauna kan wani kudiri da Birtaniyya ta zartas, wanda za a fara a farkon mako mai zuwa, game da yakin da aka kwashe kusan shekara guda ana gwabzawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun sa kai na RSF.

Mataimakin jakadan Burtaniya na Majalisar Dinkin Duniya James Kariuki ya ce suna fatan daftarin zai samu goyon bayan kasashe.

Amurka ta ce bangarorin da ke fada da juna sun aikata laifukan yaki sannan kuma kungiyar RSF ta aikata laifukan cin zarafin bil adama da yunkurin kawar da wata kabila daga doron kasa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce kusan rabin al'ummar Sudan na bukatar agaji, inda a halin yanzu mutum miliyan 8 ne suka kauracewa garuruwansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.