Isa ga babban shafi

Sojin Ghana ya mutu a aikin wanzar da zaman lafiya na MDD a Sudan ta kudu

Majalisar Dinkin Duniya ta tabbatar da mutuwar wani sojan Mali guda a Sudan ta kudu da ke cikin dakarun da ke aikin wanzar da zaman lafiya a kasar wadda ta yi fama da rikici tsawon shekaru.

Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta kudu.
Dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta kudu. © Glody Murhabazi / AFP
Talla

Sanarwar da Majalisar ta fitar, ta ce Sojan na Ghana ya rasa ransa ne a yankin Abyei mai fama da rikici a iyakar kasar da Sudan.  

Rahotanni sun ce rikici ya barke a sassa 3 na yankin Abyei tsakanin mayakan ‘yan tawaye masu rike da makamai da kuma jami’an tsaron da ke aikin wanzar da zaman lafiya a yankin.

A cewar sanarwarr Majalisar baya ga Sojin akwai kuma tarin fararen hular da suka mutu, wanda ya tilasta kwashe mutane daga sassa 3 da rikicin ya tsananta zuwa tuddan mun tsira.

Rikici tsakanin kabilun yankin na Abyei ba sabon abu ba ne lura da yadda suka shafe tsawon shekaru suna yakar juna a yankin wanda ke dauke da mabanbantan kabilu.

Yankin na Abyei mai arzikin albarkatun karkashin kasa, har yanzu ana takaddama game da hakikanin wanda ke da iko akansa tsakanin Sudan da Sudan ta kudu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.