Isa ga babban shafi

Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashen gabashin Afrika sun fara ficewa daga Jamhuriyar Congo

Dakarun rundunar wanzar da zaman lafiya na kungiyar kasshen yankin gabashin Afrika (EAC) a yau lahadi 3 ga watan decemba sun fara ficewa daga kasar JDC. Gungun farko dake kunshe da daruruwan sojojin kasar Kenya, ya fice daga garin Goma ne da misalign karfe biyar na asubahin yau lahadi, bayan da jirginsu ya cira zuwa Nairobi.

wani dakaren sojin kasar Kenya a rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasshen yankin gabashin Afrika a lokacin da suke barin kasar ra Congo  a filin saukar jiragen saman  Goma airport, on 3 December 2023.
wani dakaren sojin kasar Kenya a rundunar wanzar da zaman lafiya ta kasshen yankin gabashin Afrika a lokacin da suke barin kasar ra Congo a filin saukar jiragen saman Goma airport, on 3 December 2023. AFP - ALEXIS HUGUET
Talla

A ranar 24 ga watan Nobemba  da ya gabata ne a lokacin zaman taron kasshen yankin gabashin Afrika da aka gudanar a Tanzaniya, kasar JDC ta bayyana cewa,  ba za ta tsawaita wa’adin ci gaba da zaman dakarun  wanzar da zaman lafiyar da ke aiki  a yankin arewacin Kivu ba, wa'adin da ke kawo karshensa a ranar 8 ga wannan wata na desembar da muke ciki, a yayin da rundunar  ke ci gaba da shan suka a cikin kasar ta Congo.

Ficewar farko a karkashin matakin da zaman taron kasashen gabashin Afrika suka dauka a watan nobembar da ya gabata, da ya fara aiki ne da dakarun sojin  kasar Kenya.

A ranar juma’ar da ta gabata,  shugaban rundunar sojij kasar Kenya,   ya ziyarci garin Goma, inda ya yabawa dakarunsa,  kan irin kyakyawan aikin sadaukarwa da suka gudanar a arewacin Kivu.

Yau shekara guda ke nan,  da tawagar dakarun wanzar da hana tu'annatin da yan tawayen kungiyar M23 ke shukawa a yankin, sai dai kuma  rundunar  ta fuskanci soke soke masunauyi da ga yan kasar ta Jamhuriyar Demokradiyar Congo.

Mahukumtan  Kinshasa sun yi zargin cewa,  rundunar ba ta yi nasarar magance matsalolin da suka, sa aka aikata a yankin ba, ta yadda ta kasa saka yan tawayen na M23 aje makamansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.