Isa ga babban shafi

Sojojin Sudan sun haramta shigar da kayan agaji zuwa yankin Darfur

Hukumomin da ke biyayya ga shugaban gwamnatin sojin Sudan, Janar Abdulfatah Al-Burhan, sun kulle hanyoyin shiga Darfur, abin da ya haifar da tsaiko ga aikin  agajin da ake kai wa yankin da ke yammacin kasar.

Wasu 'yan Sudan a garin Adre, bayan da suka tsere daga yankin Darfur, yayin kokarin tsallaka iyakar kasar tasu zuwa cikin Chadi. 4 ga Agustan, 2023.
Wasu 'yan Sudan a garin Adre, bayan da suka tsere daga yankin Darfur, yayin kokarin tsallaka iyakar kasar tasu zuwa cikin Chadi. 4 ga Agustan, 2023. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Yankin na Darfur mai iyaka da kasar Chadi ya kasance daya daga cikin yankunan kasar Sudan da aka fi fama da rikici tun bayan yakin da aka gwabza watanni 10 da suka gabata tsakanin sojojin Sudan da dakarun kai daukin gaggawa na RSF.

RSF dai ta samo asali ne daga dakarun Janjaweed da suka fara yakin neman zabe a yankin Darfur fiye da shekaru ashirin da suka gabata.

A yakin da suke yi da sojoji a halin yanzu, wanda aka fara a watan Afrilun da ya gabata, RSF ta kwace ikon hudu daga cikin manyan biranen Darfur biyar.

Sama da mutane 694,000 ne suka yi gudun hijira zuwa kasar Chadi, a cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta duniya, amma wasu da dama sun makale a Darfur kuma suna bukatar taimakon gaggawa.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce dole ne ta takaita ayyukanta a yankin Darfur da kuma kan iyaka zuwa kasar Chadi, amma a makon da ya gabata daraktan hukumar samar da abinci na Majalisar, Eddie Rowe ya shaidawa manema labarai cewa hukumomi sun takaita ayyukan jin kai zuwa iyakokin Chadi.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka Matthew Miller ya ce Amurka ta damu matuka da matakin da sojojin kasar suka dauka na hana kai agajin jin kai daga kasar Chadi a baya-bayan nan da kuma rahotannin da ke cewa gwamnatin sojin ta hana kai agaji ga al'ummomin yankunan da RSF ke iko da su.

Sai dai hukumomin sojin sun ce, iyakar Sudan da Chadi ita ce babbar mashigar makamai da kayan aiki da ake amfani da su wajen aikata ta'asa ga 'yan Sudan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.