Isa ga babban shafi

Yara 13 ne ke mutuwa kowacce rana a Sudan saboda yunwa - MSF

Kungiyar likitoci ta kasa da kasa ta ce, akalla yara 13 ne, ke mutuwa kowacce rana a sakamakon tsananin cutar yunwa a sansanin Zamzam da ke arewacin Darfur na kasar Sudan, wanda hakan na da nasaba da yakin da ya barke a kasar watanni 10 da suka gabata.

Rawda Muhammad Isma'il kena da ke zaman jinyar yaronta a wani asibitin MSF da ke Chadi, bayan ta tsere daga arewacin Darfur na kasar Sudan.
Rawda Muhammad Isma'il kena da ke zaman jinyar yaronta a wani asibitin MSF da ke Chadi, bayan ta tsere daga arewacin Darfur na kasar Sudan. REUTERS - ZOHRA BENSEMRA
Talla

Shugaban hukumar kula da ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya, ya gargadi kasashen Turai da cewa su shirya karbar masu neman mafaka daga Sudan, idan har aka gaza shawo kan rikicin da ke faruwa tsakanin manyan hafsoshin kasar.

Shugabar sashen bada agajin gaggawa ta kungiyar MSF a Sudan din, Claire Nicole, ta ce, ana rasa yaro guda a cikin sa’o’I biyu ko wacce rana,

“Wadanda ke fama da tsananin cutar yunwa da har yanzu basu samu kulawar gaggawa ba, na cikin hadarin rasa ransu daga nan zuwa makonni uku ko kuma shida,” in ji Nicolet.

MSF ta ce, sansanin Zamzam, wanda ke dauke da mutane sama da 300,000, da dama daga cikinsu sun gudu ne daga wuraren da rikicin kabilanci ya daidaita a shekarar 2023.

Haka zalika, tun daga lokacin da rikici ya barke a tsakanin manyan hafsoshin SDudan a watan Afrilun 2023, aka katse hanyoyin kai agaji ga sansanonin ‘yan gudun hijira.

Hukumomin Majalisar Dinkin Duniya da kuma kungiyoyin bayar da agaji na kasa da kasa, sun janye daga arewacin Darfur, bayan da yakin ya balle a watan Afrilu.

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, ta ce idan har ba a kara rubanya hanyoyin jin kai ga ‘yan gudun hijirar Sudan ba, shakka babu za su fara yunkurin tsallakawa Turai.

Sama da mutum miliyan tara ne suka rasa muhallanssu a Sudan, kuma miliyan daya da rabi sun tsallaka zuwa kasashe makwabta a cikin watanni 10.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.