Isa ga babban shafi

Gwamman mutane sun mutu a hare-haren da aka kai coci da masallaci a Burkina Faso

Gwamman mutane ne suka mutu a wasu hare -haren da aka kai wani masallaci da kuma wata mujami’ar Katolika a safiyar Lahadi a Burkina Faso.

Gwamman mutane sun mutu a haren da aka kai coci da massalaci a Burkina Faso.
Gwamman mutane sun mutu a haren da aka kai coci da massalaci a Burkina Faso. RFI
Talla

Majiyoyi sun ce wasu mahara ne suka fara yi wa wani masallaci a garin Natiaboani na gabashin Burkina Faso kawanya a yayin da al’umma ke sallar asuba a ranar Lahadi, inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi, lamarin da ya yi sanadin mutuwar gwamman masu ibada, ya kuma jikkata da dama.

Rahotanni sun ce dukkannin wadanda suka gamu da ajalinsu a wannan masallaci maza ne, kuma cikinsu akwai wani fitaccen malamin addinin Musulunci.

A waje daya kuma, a wannan rana ta Lahadi wasu ‘yan bindiga suka kai samame wata mujammi’ar Katolika a arewacin Burkina Faso, inda suka kashe mutane 15 tare da jikkata wasu mutum biyu a yayin da suke ibadar ranar Lahadi.

Harin ya auku ne a kauyen Essakane na arewacin kasar kamar yadda wani babban jami’in majami’ar, Jean Pierre Sawadogo ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar.

Wannan shi ne harin baya baya daga cikin jerin hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa yankunan kasar. Kasar na daga cikin kasashen yankin Sahel da ke fuskantar munanan ayyukan ‘yan ta’adda tun bayan yakin Libya a shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.