Isa ga babban shafi

'Yan ta'adda sun kai mummunan hari kan rundunar Sojin Burkina Faso

Wasu majiyoyin tsaro a Burkina Faso sun tabbatar da faruwar wani mummunan harin ta’addanci da mayaka masu ikirarin jihadi suka kai kan dakarun sojin kasar ko da ya ke babu cikakkun alkaluma kan asarar rayukan da aka yi a harin.

Wasu Sojojin Burkina Faso.
Wasu Sojojin Burkina Faso. AFP - SIA KAMBOU
Talla

A cewar majiyoyin kamar yadda suka shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP yau Talata, gungun ‘yan ta’addan rike da muggan mukamai sun farmaki wani bangare na rundunar Sojin Burkina Faso da ke yankin arewacin kasar mai fama da hare-haren ta’addanci, wanda ya kai ga musayar wuta a tsakaninsu.

Majiyoyin sun ce da misalin karfe 3 na tsakar ranar Lahadin da ta gabata ne harin ya faru kuma yawan mayakan da suka kai farmakin ya haura 100, ko da ya ke dakarun na Burkina Faso sun yi amfani da jirgin yakin soji wajen mayar da farmaki.

Har zuwa yanzu ma’aikatar tsaron Burkina Faso ba ta bayar bahasi kan harin ba, sai dai majiyoyi sun ce an tafka asarar rayuka a dukkanin bangarorin biyu.

A cewar majiyoyin maharan, sun bi bayan wajen da suka kaddamar da farmaki don laluben ko akwai masu sauran lumfashi a cikinsu, amma kuma jirgin soji ya sake yi musu luguden wuta.

Ma’aikatar yada labarai ta Burkina Faso ta ce dakarun Sojin sun yi nasarar kisan ‘yan ta’adda fiye da 400 a lokacin da wani gungu na kusan mutum dubu 3 suka yi yunkurin kwace iko da garin Djibo.

Tun a shekarar 2015, Burkina Faso ke fama da hare-haren ‘yan ta’adda wanda ya kai kisan ga kisan mutane dubu 17 ciki har da Sojoji da fararen hula baya ga raba mutane miliyan 2 da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.