Isa ga babban shafi

Amnesty ta zargi 'yan ta'adda da aikata laifukan yaki a Burkina Faso

Kungiyar Kare Hakkin Bil Adama ta Amnesty International ta zargi kungiyoyin da ke dauke da makamai a Burkina Faso, cikin su harda Ansarul Islam da aikata laifuffukan yaki wajen kashe fararen hula a yankunan da suka yi wa kawanya. 

Wasu masu dauke da makamai a yankin Sahel
Wasu masu dauke da makamai a yankin Sahel © SOULEYMANE AG ANARA / AFP
Talla

Wani rahoto da kungiyar Amnesty ta fitar mai dauke da taken ‘mutuwa na jiranmu, yayin da muke zama cikin kawanyan hali a Burkina Faso’, kungiyar ta bankado yadda ake cin zarafin jama’a tare da take hakkin Bil Adama wajen hana su noma da kiwo da kuma takaita musu hanyoyin samun ilimi da kula da lafiyar su, abinda ya tilastawa dubbai daga cikin su barin gidajen da suka mallaka. 

Daraktan kungiyar mai kula da yankunan Afirka ta Yamma da Tsakiya, Samira Daoud ta zargi Ansaru da wasu kungiyoyin yankin da aikata manyan laifuffuka a fadin kasar ta Burkina Faso, yayin da take cewa bayan yin kawanya ga yankunan kasar da dama, kungiyoyin sun kuma kashe dubban fararen hula da da kuma lalata kayan more rayuwar su, ciki harda gadoji da ruwan sha. 

Hari kan fareren hula kai tsaye

Amnesty ta ce kungiyoyin na kuma kai hari a kan tawagar motocin dake dauke da kayayyaki, abinda ke shafar fararen hula kai tsaye, inda ta bayyana cewar a cikin kowadanne mutane 12 dake kasar a yau, mutum guda ya bar gidansa saboda tashin hankalin dake gudana. 

Kungiyar ta ce ya zuwa watan Yulin bana, akalla al’ummomin yankuna 46 ‘yan bindiga suka yi wa kawanya a sassan kasar, abinda ya samo assali tun daga shekarar 2019, ya kuma zama ruwan dare a wannan lokaci, ganin yadda ‘yan bindigar ke sanya shinge a hanyoyin mota, suna dasa bama bamai domin hana zirga zirga da kuma kai hari a kan fararen hula da sojoji da kuma motocin dake dauke da kayan masarufi, abinda ya kaiga shafar akalla mutane kusan miliyan guda. 

'Yan ta'adda na yi wa garuruwa kawanya

Wani shugaban al’umma ya shaidawa Amnesty cewar, ya zuwa wannan lokaci, a kowacce rana ana samun birane da kauyuka dake fama da irin wannan kawanya, cikin su harda Arbinda wanda aka masa kawanya tun daga shekarar 2019, tare da kuma garuruwa irin su Gorgadji da Solle da Mansila da kuma Titoa, abinda ke barazana ga rayukan jama’ar dake cikin su. 

Kungiyar Amnesty ta ce hukumomin Burkina Faso sun yi kokarin mayar da doka da oda, cikinsu harda daukar matakan da kan iya yiwa fararen hula illa, amma har yanzu ba a kaiga cimma nasarar da ake bukata ba. 

Dakarun gwamnati

Rundunar sojin Burkina Faso wadda ke samun goyan bayan kungiyar ‘yan Sakai ta VDP wadda aka kafa a shekarar 2020, ta kai hari a garin Holde dake kusa da Djibo wanda kungiyar Ansarul Islam ke iko da shi a ranar 9 ga watan Nuwambar bara, abinda ya kai ga hallaka fararen hula 49 akasarin su mata da yara. 

Ganin yadda matsalar ta yi kamari, a shekarar 2019 hukumomin Burkina Faso sun kafa dokar ta baci, abinda ya baiwa sojin karfin mulki a yankin, ciki harda daukar matakan samar da rakiyar motocin dake dauke da mutane da abinci tare da wasu kayayyakin dake dauke da hadari, yayin da kuma suka haramta aikewa da sakon kudade a yankin Sahel da kuma gabashin kasar, matakin da ya shafi gudanar da ayyukan jinkai ga mutanen dake bukata. 

Tsamin dangartakar kasa da kasa

Lalacewar dangantaka tsakanin hukumomin sojin kasar da kuma masu aikin jinkai ta sa aka kori jami’in jinkai na majalisar dinkin duniya a watan Disambar shekarar 2022, abinda ya haifar da matukar illa ga akalla yan kasar Burkina Faso miliyan 2 dake bukatar taimako. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.