Isa ga babban shafi

Amnesty ta bukaci Burkina Faso ta kawo karshen muzgunawa kafafen yada labarai

Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International ta bukaci sojojin da ke mulkin Burkina Faso da su dakatar da cin zarafi gami da barazanar da suke yi wa wasu kafafen yada labarai. 

Wani mutum a gidansa yayin da ke kallon talabijin sa'o'i bayan da sojojin Burkina Faso suka dakatar da kafar talabijin ta France24, a ranar 27 ga watan Maris na shekara ta 2023.
Wani mutum a gidansa yayin da ke kallon talabijin sa'o'i bayan da sojojin Burkina Faso suka dakatar da kafar talabijin ta France24, a ranar 27 ga watan Maris na shekara ta 2023. AFP - OLYMPIA DE MAISMONT
Talla

Kiran kungiyar dai ya zo ne bayan da shugaban hukumar kare hakkin bil’adama na majalisar dinkin duniya Volker Turk ya ce ya kadu matuka game da karuwar take hakkin dan adam da kuma take 'yancin manema labarai da sojojin na Burkina Faso ke yi. 

Samira Daoud daraktar kungiyar da ke kula da yammacin Africa ta Amnesty, ta ce lokaci ya yi da Burkina Faso za ta gane cewa kasancewar ta karkashin mulkin soja ba ya nufin suna da damar cin zarafin al’umma yadda suke so ba. 

A cewar Samira, sallamar 'yan jarida da hana su gudanar da ayyukansu a dai-dai lokacin da kasar ke ikirarin yaki da 'yan ta’adda abu ne mai matukar hatsari, da kuma tauye wa mutane hakkin samun bayanai da suke da shi. 

A makon da ya gabata ne dai Burkina Faso ta sallami wasu ma’aikatan Jaridar Farasan guda biyu daga kasar, inda ta basu wa’adin sa’o’i 24, abinda ke zuwa mako guda tak bayan ta dakatar da ayyukan kafar talabijin ta France24. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.