Isa ga babban shafi

Bukina Faso ta dakatar da ayyukan France 24 a kasar

Gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso ta sanar da dakatar da kafar yada labarai ta France 24 daga yada shirye-shiryen ta a kasar, bayan wata hira da suka yi da shugaban kungiyar Al-Qaeda na shiyar arewacin Afirka Abu Ubaydah Yusuf al-Annabi.

Tambarin France 24.
Tambarin France 24. France24.com
Talla

Tun a shekarar 2015 ne Burkina Faso ta fara yaki da masu ikirarin jihadi, da su ka kutsa cikin kasar daga makwabciyar ta Mali.

Kakakin gwamnatin sojin Burka Faso Jean Emmanuel Ouedraogo ne sanar da matakin na su, inda ya ce kalaman da shugaban na Al-Qaeda ya yi sun saba ka’ida kuma suna tattare da tunzurawa jama'a.

Ko a watan Disambar shekarar da ta gabata, sai da gwamnatin sojin Burkina Faso ta dakatar da gidan Radio France International RFI wanda dukkanin su ke karkashin France Medias Monde group, bayan zargin gidan radion da yada kalaman jagoran ‘yan ta’addan da ke tattare da tunzurawa.

Duk kanin RFI da kuma France 24 da ke bibiyan al’amuran da ke gudana musamman a kasashen da Faransa ta yiwa mulkin mallaka a Afrika sau da kafa, gwamnatin mulkin sojin Mali da ke makwabtaka da Burkina Faso ta dakatar da su daga yada shirye-shiryen su daga kasar,  bayan da suka zargi sojojin kasar da cin zarafin fararen hula.

Gwamnatin Ouagadougou ta ce za ta ci gaba da yin dukkanin abinda ya kamata wajen kare al’ummar ta daga duk wasu masu kokarin kawo rarrabuwar kai ta hanyar kalaman batanci a kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.