Isa ga babban shafi

Kafofin labaran Burkina Faso sun yi tir da matakin dakatar da RFI a kasar

Gamayyar kafofin yada labarai a Burkina Faso sun zargi gwamnatin da ke mulkin kasar da rashin kyautawa wajen dakatar da gidan radiyon Faransa RFI wanda da aka fi saurare a kasar da ke yankin Sahel.

dakatar da kafar yada labaran ta RFI ya haddasa cece-kuce da ita.
dakatar da kafar yada labaran ta RFI ya haddasa cece-kuce da ita. © rfi
Talla

A cikin sanarwar da kafofin yada labaran kasar 10 suka fitar, sun ce kafofin yada labarai na fuskantar matsin lamba sosai daga hukumomin kasar.

A ranar 3 ga watan Disamban nan ne gwamnatin sojin kasar ta umarci kafar yada labarai ta RFI ta daina yada shirye-shiryen ta a kasar, bisa zargin ta da yada kalaman barazana da jagoran ‘yan ta’addan kasar ya yi.

Sai dai sanarwar da kafofin yada labaran suka fitar sun nuna goyon bayan su dari bisa dari ga kafar ta RFI da kuma bayyana cewar an sanya siyasa a game da batun dakatarwar.

Burkina Faso dai ta kwashe tsawon shekaru 7 ta na yaki da masu ikirarin jihadi, wanda ya lakume rayukan mutane da dama tare kuma da tilastawa kimanin mutane miliyan biyu barin gidajen su.

Tashe-tashen hankalin da ake fuskanta a kasar dai ya haifar da juyin Mulki har sau biyu a cikin wannan shekarar, na karshe shi ne wanda aka yi a ranar 30 ga watan Satumbar da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.