Isa ga babban shafi

Burkina Faso ta baiwa wani kamfanin Rasha lasisin hako zinare

Gwamnatin Sojin Burkina Faso ta baiwa wani kamfanin hakar ma’adinan Rasha da ake kira Nordgold lasisin hako zinare a cikin kasar. 

Wani wurin hakar gwal
Wani wurin hakar gwal REUTERS - XXSTRINGERXX xxxxx
Talla

Sanarwar da gwamnati ta fitar yau alhamis yace lasisin na shekaru 4 zai baiwa kamfanin damar hako ma’adinin a Yimiougou dake tsakiyar yankin arewacin kasar, kuma ana saran hako akalla tan biyu da rabi na zinare a wurin. 

Gwamnatin kasar tace tana saran samun kudaden da zasu kai Dala miliyan 8 da rabi daga kamfanin, abinda zai bata damar kara kasafin kudinta. 

Tuni kamfanin Nordgold ke aiki a wasu wurare guda 3 tare da wasu kamfanonin cikin gida a yankin arewacin kasar dake fama da ayyukan ta’addanci tun daga shekarar 2015. 

Zinare ne ma’adini na gaba dake samarwar Burkina Faso kudaden shiga, kafin auduga wanda ke matsayi na biyu. 

Kasar Rasha na ci gaba da samun farin jinni a kasashen Afirka renon Faransa, yayin da ake sukar Faransa da ta musu mulkin mallaka. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.