Isa ga babban shafi

Burkina Faso za ta tara Yuro miliyan 152 domin magance matsalar tsaro

Gwamnatin Burkina Faso ta sanar da shirin tara Yuro miliyan 152 don domin tunkarar rikice-rikicen masu tada kayar baya da ke addabar kasar.

Sojojin Burkina Faso kenan ranar 7 ga Maris, 2018, a Ouagadougou, yayin bikin tunawa da wasu ma'aikatan Burkina Faso guda takwas da aka kashe a wasu tagwayen hare-hare.
Sojojin Burkina Faso kenan ranar 7 ga Maris, 2018, a Ouagadougou, yayin bikin tunawa da wasu ma'aikatan Burkina Faso guda takwas da aka kashe a wasu tagwayen hare-hare. AFP via Getty Images - AHMED OUOBA
Talla

Ya kamata asusun ya ba mu damar tara CFA biliyan 100 a shekara ta 2023, in ji Ministan Tattalin Arziki Aboubacar Nacanabo bayan tattaunawa da Shugaba Ibrahim Traore.

A matsayin wani bangare na yaki da ta'addanci, gwamnati ta yanke shawarar daukar ma’aikatan saka kai 50,000 don kare kasarmu," in ji ministan.

Ya kara da cewa, za a rika biyan masu taimakawa farar hula da ke tallafa wa sojoji 60,000 na CFA a kowanne wata, ko kuma Yuro 91.

"Bayan wannan kudin, dole ne a siyo makamai don ba su kayan aiki, da za su yi amfani da su, motoci, man fetur da sauran su," in ji Nacanabo.

Har ila yau, ya bayyana cewa kashi daya bisa dari na kowanne albashi, ciki har da na 'yan majalisar dokoki, da harajin tallace-tallace kan abubuwan sha, sigari, intanet, da kayan alatu za a rika cirewa ne domin taimakawa wajen biyan kudaden da ake kashewa a yakin da ya yadu daga Mali zuwa kasar tun 2015.

Firaminista Apollinaire Kielem de Tembela a makon da ya gabata ya nemi Faransa da ta taimakawa kasar da makamai da alburusai don magance ayyukan ta’addanci.

An kafa rundunar sa kai ta VDP a karshen shekarar 2019 da ke karbar horon aikin soji na tsawon makonni biyu.

Amma an kashe daruruwan masu aikin sa kai a harin kwantan bauna ko kuma ta hanyar dasa bama-bamai a gefen hanya.

Duk da asarar rayuka da aka samu, mutane 90,000 ne suka yi rajista karkashin wani shirin daukar ma'aikata na VDP a watan Nuwamba, a cewar hukumomi.

Burkina Faso dai ta fuskanci juyin mulkin soji sau biyu a wannan shekara, sakamakon fusata sojoji suka yi saboda gazawar da aka samu wajen magance matsalolin masu dauke da makamai.

Sai dai adadin hare-haren da ake dangantawa da kungiyar IS da Al-Qaeda ya karu a 'yan watannin nan, musamman a arewaci da gabashin kasar da ke tsakiyar yankin Sahel.

Kyaftin Ibrahim Traore, wanda ya karbi ragamar shugabancin kasar bayan juyin mulki a ranar 30 ga watan Satumba, ya bayyana aniyarsa ta sake kwato yankunan da gungun 'yan ta'adda suka mamaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.