Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya hallaka 'yan kato da gora 12 a Burkina Faso

Akalla mutane 12 ne suka rasa rayukansu mafi yawansu jami’an tsaron sa-kai da ke taimaka wa dakarun gwamnatin Burkina Faso, sakamakon harin da ‘yan bindiga suka kai a arewacin kasar.

Sojoji na sintiri a birnin Ouagadougou na Burkina Faso. 30/09/22.
Sojoji na sintiri a birnin Ouagadougou na Burkina Faso. 30/09/22. © Olympia de Maismont / AFP
Talla

‘Yan bindigar sun kai hari ne kan wani garin mai suna Boala da ke lardin Arewa ta Tsakiya, inda suka kashe mutane 12, kuma dukannin mamatan ‘yan sa-kai ne da ke taimaka wa jami’an tsaron kasar ta Burkina Faso.

Hakazalika shaidu sun tabbatar da cewa akwai wani adadi na mutane masu tarin yawa da aka kwantar a asibitin garin Boulsa da ke matsayin shalkwatar lardin Namentenga, saboda raunukan da suka samu.

Wani jami’in gwamnati a yankin wanda bai bukaci a bayyana sunansa ba, ya tabbatar da faruwar lamarin. sai dai ya ce bayan share tsawon sa’o’i ana artabu, ‘yan bindiga da dama sun rasa rayukansu.

Daga ranar lahadi zuwa Alhamis, wannan ne karo na hudu da ‘yan bindiga ke kai hare-hare a sassan kasar ta Burkina Faso, tare da haddasa asarar rayukan akalla mutane 27.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.