Isa ga babban shafi

Yan ta'adda sun kashe sojojin Burkina Faso 13

Sojoji 13 ne aka kashe a jiya asabar a wani harin kwantan bauna da masu ikirarin jihadi  suka kai a gabashin kasar Burkina Faso, kamar yadda majiyoyin tsaro suka shaida wa kamfanin dillancin labaran Faransa a yau Lahadi.

Dakarun kasar Burkina Faso  a arewacin kasar
Dakarun kasar Burkina Faso a arewacin kasar © AFP
Talla

Majiyar tsaro ta ce, wani bangare na jami’an tsaro , da ke yankin Fada N’Gourma da Natiaboani a gabashin kasar ne aka yi musu kwanton bauna. Majiyar ta kara da cewa sojoji 13 ne suka mutu sannan hudu suka samu raunuka.

Wannan harin dai na zuwa ne jim kadan bayan harin da aka kai a ranar litinin a Djibo, wani babban birni a arewacin kasar Burkina Faso da ke karkashin ikon mayakan jihadi na tsawon watanni uku, inda aka kashe sojoji goma tare da jikkata 50.

Tun daga shekara ta 2015, sojojin Burkina Faso ke fama da tashe-tashen hankula a kai a kai sakamakon yawaitar hare-haren 'yan jihadi da suka yi sanadiyar mutuwar dubban mutane tare da tilastawa wasu mutane miliyan biyu barin gidajensu.

Wadannan hare-hare sun yawaita a cikin ‘yan watannin nan, musamman a arewaci da gabashin kasar.

Shugaban rikon kwarya da majalisar tsarin mulkin kasar ta nada a ranar 21 ga watan Oktoba, Kyaftin Ibrahim Traoré, wanda ya hambarar da Laftanar-Kanar Paul-Henri Sandaogo Damiba  ranar 30 ga watan Satumba, ya dau alkawalin dawo da doka da oda a wasu yankunan kasar ta Burkina faso.

A ranar Laraba da ta gabata, majalisar sojin kasar ta  kudiri aniyar daukar ma'aikata kusan 50,000 masu aikin sa kai na Tsaron Gida (VDP), da za su taimakawa sojojin, a cikin tsarin yaki da ta'addanci a Burkina Faso.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.