Isa ga babban shafi

Gwamnatin sojin Burkina Faso za ta sabunta kundin tsarin mulki

Jagoran juyin mulkin Burkina Faso, Kyaftin Ibrahim Traoré, zai kira wani babban taro a ranakun 14 da 15 ga watan Oktoba domin cimma yarjejeniyar mika mulki.

Sabon shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso Ibrahim Traoré kenan daga tsakiya
Sabon shugaban gwamnatin sojin Burkina Faso Ibrahim Traoré kenan daga tsakiya AFP - ISSOUF SANOGO
Talla

Sanarwar ta zo ne a ranar Asabar bayan karanta wata doka a gidan talabijin na kasar.

Ana shirin gudanar da taron majalisar a birnin Ouagadougou, a wannan lokacin ne za a amince da wata yarjejeniya wadda za ta bayyana matakan da kasar za ta dauka wajen gudanar da zabe. A cewar gidan rediyon kasar Omega, taron zai tattaro masu ruwa da tsaki da suka hada da kungiyoyin farar hula da masu rike da mukaman siyasa.

Masu tayar da kayar baya sun kashe dubban mutane tare da tilastawa wasu miliyan 2 barin gidajensu tun daga shekarar 2015.

Duk da ayyukan soji, hare-haren sun karu tun tsakiyar watan Maris kuma suna ci gaba da jefa iyalai da dama cikin dimuwa.

"Ayyukan ta'addanci yana jefa al'ummar Burkina Faso cikin wahala", in ji kawun wani sojan da aka kashe.

"Muna tare da sabon shugaban kasar kuma muna addu'ar Allah ya taimake shi sannan kuma muna neman kayan aiki da ma'aikata domin mu fita daga cikin wannan lamarin, idan ba haka ba, 'ya'yanmu da yawa za su mutu," in ji Moumouni Zoundi.

Zoundi na daya daga cikin wadanda suka halarci jana'izar sojoji 27 da aka kashe a ranar Asabar 26 ga watan Satumba. Kyaftin Ibrahim Traoré shima ya halarci jana'izar.

Sojojin 27 na cikin ayarin motocin dakon kaya sama da 200 da ke kan hanyar zuwa garin Djibo, babban birnin yankin arewacin kasar, a lokacin da aka kai musu farmaki.

Baya ga su, akalla fararen hula 10 ne suka mutu, wasu kuma har yanzu ba a san inda suke ba.

Kungiyar ta'addanci ta Al Qaeda ta dauki alhakin kai harin. Ana kallon wannan koma baya na soji a matsayin wanda ya kawo juyin mulki na 2 a kasar da ke yammacin Afirka.

Jim kadan bayan hawansa karagar mulki, shugaba Traoré ya yi zargin cewa sojoji ba su da tsarin dabaru a karkashin magabacinsa Damiba. Abin jira a gani shine ko zai iya juya al’amarin zuwa ga matakin nasara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.